Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya
habarta cewa: wannan Jaridar Ibrananci Yediot Aharonot ta kawo shafinta cewa:
manyan rundunonin Isra’ila biyar da wasu rukunin rundunoni biyu na kota kwana
ba su iya mamaye ƙauye ɗaya a kudancin Lebanon cikin makonni huɗu ba.
A halin da ake ciki dai, wannan adadin dakarun soji ya ninka adadin wadanda suka halarci yakin kwanaki 33 har sau 3.